Maras Hoto
Search

 
Janar David Petraeus Da Jakada Ryan Crocker Sun Bayar Da Shaida Game Da Yakin Iraqi

08/04/2008

Janar Petraeus (hagu) da Jakada Ryan Crocker a damaBabban kwamandan sojojin Amurka a Iraqi ya bayyana dari-darin ajiye lokaci na janyewa daga Iraqi, yana mai fada wa majalisar dokoki cewa ci gaban da aka samu bai zauna sosai yadda ya kamata ba.

Janar David Petraeus ya fadawa Kwamitin Kula da Ayyukan Soja na Majalisar Dattijai a yau talata cewa ya kamata Amurka ta janye karin sojoji dubu 30 da ta tura Iraqi a shekarar da ta shige nan da watan Yuli. Amma yace daga nan, ya kamata kwamandojin dake can su nazarci halin tsaro na wasu kwanaki 45 kafin a yanke shawarar ko za a iya maido da karin sojoji gida.

Janar Petraeus da jakadan Amurka a Iraqi, Ryan Crocker suna bayar da shaida a gaban kwamitocin majalisar dokoki yau talata da kuma gobe laraba. Crocker, a nasa bangaren, yayi gargadin cewa sauya alkiblar manufofin Amurka na yanzu a Iraqi na iya kawo faduwa.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
An Kama Radovan Karadzic

  Karin Labarai
Sabuwar Gasar Kacici-Kacici Ta 2008
Taron Kasashe Masu Arzikin Masana'antu Zai Mayar Da Hankali Kan Sauyin Yanayi Da Wasu Batutuwan
Taron Kolin Kasashen Afirka yayi Kiran Da A Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Zimbabwe
Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka Zata Fara Taron Koli Yau Litinin