Maras Hoto
Search

 
Somaliyawa Shida Sun Isa Faransa

16/04/2008

Jirgin ruwan shakatawa na Faransa 'Le Ponant,' wanda 'yan fashi suka shige shi.Jami’ai sun ce wasu Somaliyawa da ake zargin cewa ’yan fashi cikin teku ne su 6, wadanda kuma ake zargi da yin fashin wani jirgin ruwan shakatawa na Faransa a kusa da gabar Somaliya sun isa kasar Faransa inda za a gurfanar da su gaban kotu.

A yau laraba aka kai mutanen shida Faransa a cikin wani jirgin saman soja, kuma nan take aka damka su hannun hukumomin kurkuku.

Sojojin Faransa sun damke mutanen ranar jumma’a a cikin Somaliya a bayan da aka sako ma’aikatan jirgin ruwan su 30 da aka yi garkuwa da su. 22 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su Faransawa ne.

Jami’an Faransa sun jira sai da suka samu izni daga hukumomin Somaliya kafin kai mutanen Faransa don yi musu shari’a.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Taron Kolin Kasashen Afirka yayi Kiran Da A Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Zimbabwe

  Karin Labarai
Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka Zata Fara Taron Koli Yau Litinin
Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya yayi Tur Da Cin Zarafin 'Yan Hamayya Da Ake Yi A Zimbabwe
Morgan Tsvangirai Ya Janye Daga Zaben Fitar Da Gwani Na Shugaban Kasa A Zimbabwe
Sojojin Gwamnatin Afghanistan Da Na NATO Su Na Yakar 'Yan Taliban A Kandahar
Sangandale Rabonta Ya Rantse  Audio Clip Available