Maras Hoto
Search

Jam'iyyar Hamayya Ta Kasar Zimbabwe Ta Yi Alkawarin 'Binne' Robert Mugabe

18/05/2008

Shugaban jam'iyyar MDC, Morgan TsvangiraiBabbar jam'iyyar hamayya ta kasar Zimbabwe ta yi alkawarin "binne" shugaba Robert Mugabe a zaben fitar da gwani da za a gudanar ranar 27 ga watan Yuni.

Jam'iyyar "Movement for Democratic Change", ko MDC a takaice, ta yi wannan alkawarin a lokacin da ta ke kaddamar da yakin neman zabe a wajen wani gangamin da ta gudanar a birnin Bulawayo.

A lokacin da yake jawabi ga magoya baya su kimanin dubu goma, mataimakin shugaban jam'iyyar MDC, Thokozani Khupe, ya ce jam'iyyar zata lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da ratar da ta fi wadda ta ba Mugabe a zaben farko.

An gudanar da wannan gangami ba tare da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta MDC, Morgan Tsvangirai, ba a saboda ya jinkirta komawarsa kasar a dalilin makarkashiyar da aka yi zargin ana kullawa ta kashe shi. Gwamnatin Zimbabwe ta ce wannan zargin ba ya da tushe, kuma Mr. Tsvangirai yana neman samun wata moriyar siyasa ce kawai cikin sauki daga irin wannan zargin.

A zaben fitar da gwanin da za a gudanar, Mr. Tsvangirai yana fatar doke shugaba Mugabe wanda ya shafe shekaru 28 yana mulkin kasar Zimbabwe.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Labarai Masu Alaka
Morgan Tsvangirai Ya Fasa Komawa Zimbabwe Asabar Din Nan
 
  Muhimmin Labari
Manyan Kasuwannin Hannayen Jarin Duniya Sun Fara Farfadowa

  Karin Labarai
Kuri'ar  Neman Jin Ra'ayin Jama'a Ta Nuna Obama Kan Gaba Da Abokin Hamayyar sa John McCain,Ana Sauara Mako Uku Ayi Zabe
Manyan Kasashen Duniya Masu Hanu Da Shuni Suna Taro A Washinton Kan Matsalar Tattalin Arzikin Duniya
An Saki 'Yan Kasar Filipino Biyar Da Aka Sace a Yankin Niger Deltan Najeriya
Fitaccen Masani Kan Tattalin Arziki,Dan Amerika Krugman,Ya Sami Lambar Yabo Ta Nobel
Mutane Goma Sha Biyar Sun Halaka a Pakistan,Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake
Siyasar Amurka Tana Kara zafi
Manyan bankunan Duniya Sun Rage Kudin Fito Domin Hana Tattalin Arziki Durkushewa
'Tsagerun Niger Delta Suna Barazanar Tada Husma
`Yan takarar Shugabancin Amurka Sunyi Muhawara Ta Biyu
Bata Sake Zani Ba Sosai  A Kasuwannin Saida Hannayen Jari Duniya A Yinin Talata
‘Yan Takarar Shugabancin Amurka Sun Dau Zafi         
Kasuwannin Hannayen Jari Sun Fadi Wanwar
Makomar Wasu Cibiyoyin Kudi Ta Sa Manyan Kasuwannin Saida Hannayen Jarin Duniya Zuna Zubar Gado Daya Bayan Daya
A Daren Alhamis Din Nan ne Masu Takarar Mataimakan Shugaban Kasar Amurka Biden da Palin Zasu Kara a St Louis Dare Alhamis Din Nan
Majalisar Dattijan Amurka Zata Yi Muhawara  Kan Daftarin Ceto Tattalin Arzikin Kasar
Yau ake sa ran yin muhawarar farko tsakanin ‘yan takarar shugabancin Amurka Barack Obama,da abokin karawar sa na Republican John  McCain
Sojojin Nijeriya Su Na Gwabza Kazamin Fada Da 'Yan Tsageran Niger Delta