Sanata Barack Obama ya zamo dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat a nan Amurka.
Sanata Obama, mai shekaru 46 da haihuwa, wanda karonsa na farko ke nan da zamowa dan majalisar dattijai daga jihar Illinois, yayi magana a gaban dubban magoya bayansa cikin daren talata a birnin St. Paul a Jihar Minnesota, a cikin dakin taron da 'yan jam'iyyar Republican zasu tabbatar da John McCain a zaman dan takararsu a cikin watan Satumba.
Obama shi ne bakar fata na farko da ya zamo dan takarar shugaban kasa na wata babbar jam'iyya a tarihin Amurka. Jiya talata ya samu wakilai da suka zarce dubu biyu da dari daya da goma sha takwas da ake bukata don zamowa dan takara, a bayan da ya samu karin goyon bayan wakilai masu zaman kansu, ya kuma doke abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton a daya daga cikin jihohi biyun da suka gudanar da zabe jiya talatar.
Obama, wanda ya lashe zaben karshe na Jihar Montana, ya yabawa Uwargida Clinton a zaman jagorar da ta karfafa fata a zukatan miliyoyin jama'a.
Ita ma Clinton, wadda ta lashe zaben Jihar Dakota ta Kudu, ta yaba ma Obama a lokacin jawabin da ta yi a New York. Amma kuma ta ki yarda ta yarda cewar ta sha kaye, tana mai fadin cewa zata tuntubi magoya bayanta da shugabannin jam'iyya kafin ta yanke shawara.