Maras Hoto
Search

Taron Kolin Kasashen Afirka yayi Kiran Da A Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Zimbabwe

02/07/2008

Shugaba Robert Mugabe A Wurin Taron Kolin Kasashen AfirkaKungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta amince da wani kuduri wanda yayi kiran da a kafa gwamnatin hadin kan kasa a Zimbabwe, a bayan zaben da aka yi ta tofin Allah tsine kansa na shugaba Robert Mugabe. Haka kuma shugabannin kungiyar dake ganawa cikin sirri a Masar, sun bukaci da a ci gaba da shiga tsakanin gwamnatin Zimbabwe da 'yan hamayyar kasar.

Talata aka amince da wannan matakin a bayan da kasar Botswana ta gabatar ad wata sanarwa mai zafin lafazi wadda ta nemi da a kori Zimbabwe daga tarurrukan Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka da na Kungiyar Raya Kasashen Kudancin Afirka. Mataimakin shugaban Botswana, Mompati Merafhe, ya ce zaben fitar da gwani na makon jiya a kasar Zimbabwe bai tabbatar da halalcin gwamnatin shugaba Robert Mugabe ba.

Jami'an diflomasiyya a taron da aka yi cikin sirri, sun ce su ma shugabannin kasashen Nijeriya da Liberiya da Saliyo sun yi magana da lafazi mai karfi kan rashin halalcin zaben na Zimbabwe.

Wani kakakin gwamnatin Masar, Hossam Zaki, ya ce shugaba Mugabe yayi jawabi mai tsawo lokacin taron, inda ya fito da kakkausar harshe sukar kasashen Afirka da suka soki lamirinsa.

Tun fari talatar nan, shugabannin jam'iyyar hamayya ta MDC da na jam'iyyar ANU-PF mai mulkin kasar sun nuna cewa ba su da sha'awar ci gaba da tattaunawar siyasa. A cikin wata sanarwar da aka bayar a Harare babban birnin kasar, sakatare janar na jam'iyyar MDC, Tendai Biti, ya ce zaben bogi da aka ce an gudanar ranar 27 ga watan Yuni ya kawar da duk wata damar zaunawa don warware rikicin siyasar Zimbabwe.

Shi ma da yake magana a wurin taron kolin Kasashen Afirka a Masar, kakakin shugaban Zimbabwe, George Charamba, yayi watsi da kiraye-kirayen kafa gwamnatin hadin guiwa irin wadda aka yi a kasar Kenya, yana mai fadin cewa ai Zimbabwe ba Kenya ba ce.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Labarai Masu Alaka
Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka Zata Fara Taron Koli Yau Litinin
 
  Muhimmin Labari
Yau Laraba  taron Jam’iyyar Republican zata ayyana tsaida dan takarar shugaban kasa John McCain,da matai makiyar sa Sarah Palin.

  Karin Labarai
Yau Talata Jam’iyyar Republican ta Amurka zata fara aiwatar da shirye shiryen taron ta na kasa gadan gadan
Ruwa na pantsama ya tsallaka  manyan katangu da aka gina a New Orleans
Barack Obama ya anshi zabin da jamiyyar sa ta democrat tayi masa na zama dan takarar shugaban kasa
A yammacin Alhamis din nan ne, dan takarar shugabancin Amurka na Jam’iyyar Democrat, Barack Obama,zaiyi na’am da tsaida shi dan takara
Hillary Clinton ta kirayi illahirin ‘Yan ‘Jam’iyyar Democrat, su marawa Obama
Michelle Obama, matar dan takaran jam’iyyar Democrat, ta  gayawa mahalarta taron cewa Obama zai zamar wa Amurka hazikin shugaba
Yau litinin dinnan abude babban taron Jam’iyyar Democrat a Denver, jihar Colorado
A daren yau Laraba  taron Jam’iyyar Republican zata ayyana tsaida dan takarar shugaban kasa John McCain,da matai makiyar sa Sarah Palin.
Tsohon firayim ministan kasar Pakistan ,Nawaz Sharif, ya yanke sabon lokacin dawo da manyan alkalan kasar
Jam’iyyar Democrat ta Amurka, a makon gobe, zatayi taron ta na kasa a Denver,Colorado.
Masana Kimiyya Sun Gano Kaburburan Mutanen Zamanin Da Cikin Hamadar Sahara A Nijar
Gasar Kacici-Kacici Ta 2008
Wani Maganin Tarin Fuka Yana Rage Karfin Maganin Kashe Kaifin Cutar Kanjamau
Yau Litinin Jacob Zuma Zai Bayyana Gaban Kotu A Afirka Ta Kudu
Steve Lucas Yayi Ban Kwana Da Muryar Amurka  Audio Clip Available
Hukumomin Kasar Chile Sun Sa Idanu Kan Wasu Duwatsu Biyu Masu Aman Wuta