Shugaba Barack Obama Ya Fara Ziyararsa Ta Farko A Nahiyar Asiya
Marubuci Ibrahim Alfa Ahmed 13/11/2009
Shugaba Obama lokacin da yake tashi zuwa Asiya
Shugaba
Barack Obama na Amurka yana kan hanyarsa ta zuwa Tokyo a kasar Japan, a bayan
da yayi jawabi ga sojojin Amurka a wani sansanin mayakan sama dake birnin
Anchorage a Jihar Alaska, jihar da ta fi girma kuma ta ke kuryar arewacin Amurka.
Mr. Obama ya fadawa sojoji a sansanin mayakan sama na Elmendorf cewar ba zai ja
kafa ba wajen yin amfani da karfi domin kare Amurka da muradunta, amma kuma ba
zai jefa rayukan sojoji cikin hatsari ba sai idan hakan ya zamo dole. Yace
Amurka zata goyi bayan sojojinta a kasashen waje, da kuma iyalansu a nan gida.
Haka kuma ya lura cewa da yake yanzu ya ziyarci Jihar Alaska, ke nan ya ziyarci
dukkan jihohi hamsin na Amurka.
Shugaba Obama ya fadawa ‘yan jarida kafin ya
bar nan Washington cewa zai tattauna da shugabannin duniya a kan yadda za a
kara bude kasuwannin kasashen Asiya da na yankin tekun Pacific ga kayayyakin da
Amurka take sarrafawa.