Maras Hoto
Search

 
An Kashe Yangwagwarmaya Talatin Da Takwas a Iraqi

28/04/2008

Iraqi soldiers talk to woman as she leaves through checkpoint from Shi'ite enclave of Sadr City, Baghdad, 8 Apr 2008
Rundunar mayakan Amurka a Iraqi tace dakarun ta dana Iraqi sun kashe ‘yan gwagawarmaya 38 a Bagadaza, a wani bata kashin da ta ce shine mafi muni da aka gwabza a cikin ‘yan makonnin nan. Rundunar ta fada litinin din nan, cewa ‘yan bindiga sun fake da guguwar Hamada da ta lullube fadar kasar jiya lahadi wajen kai jerin hare hare. Guguwar ta hana jiragen yaki masu saukar ungulu aiki, wadanda sune manyan makaman da sojojin Amurka suke amfani da su a farautar mayakan sakai masu harba rokoki.

Akasarin fada a jiya a unguwar Sadr akayi, inda nanne tungar mayakan sakai masu biyayya ga shehin ‘yan mashabar shi’a Muqtada al-Sadr. A fada mafi muni mayakan Amurka da na Iraqi sun tilastawa wadanda suka kawo kazamin hari kan wata cibiyar binciken ababan hawa jada baya.

Dakarun Amurka sunce mutum ashirin da biyu cikin mayakan sakai ne aka kashe,ita Amurka da Jami’an Tsaron Iraqi ba a musu hasara ba sam.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Sabuwar Gasar Kacici-Kacici Ta 2008

  Karin Labarai
Taron Kasashe Masu Arzikin Masana'antu Zai Mayar Da Hankali Kan Sauyin Yanayi Da Wasu Batutuwan
Taron Kolin Kasashen Afirka yayi Kiran Da A Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Zimbabwe
Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka Zata Fara Taron Koli Yau Litinin
Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya yayi Tur Da Cin Zarafin 'Yan Hamayya Da Ake Yi A Zimbabwe