Koma Ga Shafi Mai Hoto

VOANews.com
News in 44 languages


 
Andakatar da zaman shawarwarin kawo zaman lafiyar  Sudan

20/10/2005

Darfur SPLA
Mashawarta dake tattaunawa domin kawo zaman lafiya tsakanin bangarorin kasar Sudan dake gaba da juna sun dage zaman tattaunawarsu a dai-dai lokacin da aka sami karin tashe tashen hankula a yankin Dafur din.  Tashin hankali na baya bayan nan sun dakatar da shirye shiryen kai kayakin agaji a yankin. Ana sa rai sai ranar 20 ga watan gobe na Nuwamba ne za’a sake komawa zauren taron wanda Kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta shirya shi tsakanin gwamnatin kasar Sudan da kungiyoyin ’yan tawayen kasar. Taron farko da aka yi wata guda ana yinsa a Nigeria bai cimma wata nasarar kirki ba, musamman a bangaren rabon arzikin kasa da rabe raben mukamai. Yake-Yake da kuma a  kai hare hare kan sojojin kiyaye zaman Lafiya na kasashen Afrika, sun dusasa zaman tattaunawar. A wannan makon MDD tace hare haren nan suna hana ayyukan agaji cigaba yayinda ala tilas suka tilatawa fararen hula yin hijira zuwa sansanonin da suke cike da mutane.

Muhimmin Labari
Jami'an Sojan Iran Sun Ce An fara Wata Gagarumar Rawar Daji Ta Kare Kasa Daga Hari Ta Sama

Karin Labarai
Yau Litinin Majalisar Dinkin Duniya Zata Kaddamar Da Aiki Mafi Girma Na Rigakafin Cutar Shawara Da Ta Taba Yi
Kwallon Kafa Ya Haddasa Rikicin Diflomasiyya Tsakanin Masar Da Aljeriya
Somaliyawa 'Yan Fashi A Teku Sun Sake Kai Hari Kan Wani Jirgin Ruwan Amurka Da Suka Taba Kamawa
Yau Alhamis Za A Rantsar Da Shugaba Hamid Karzai Na Afghanistan