Maras Hoto
Binciko Mini

 
Ma'aikatan Jinya A Tsibirin Java Sun Ce Su Na Ci Gaba Da Kokarin Jinyar Dubban Mutanen Da Suka Ji Rauni...

29/05/2006

Ana jinyar mutane a wajeMa'aikatan kiwon lafiya a tsibirin Java wanda girgizar kasa ta yi wa kaca-kaca a kasar Indonesiya sun ce su na ci gaba da gwagwarmayar jinyar dubban mutanen da suka ji rauni, yayin da wasu dubban suke ci gaba da kwarara zuwa asibitocin da tuni suka cika har suka batse. A yanzu likitoci su na gudanar da kananan ayyukan tiyata a sararin subhana.

A lardin Yogyakarta inda girgizar ta fi shafa, inda kuma da yawa daga cikin mutane kimanin dubu biyar suka rasa rayukansu, ma'aikatan agaji sun ce sun fara karancin abinci, da ruwan sha da magunguna.

Jami'an kasar Indonesiya sun yi kiyasin cewa mutane kusan dubu metan sun rasa gidajensu a girgizar kasa mai karfin awu 6 da digo uku a ma'aunin motsin kasa na Richter, wadda aka yi a yankin ranar asabar. An ce da yawa daga cikin mutanen yanzu sun jeru a kan titunan birnin Yogyakarta su na barar abinci da kayan masarufi.

Kayayyakin agaji daga kasashen waje sun fara shiga yankin, inda kungiyoyin agaji suka kai wasu kayayyakin a cikin motocin jigilar kayayyaki. Shugaba Susilo Bambang Yudhoyono ya kafa sansani a birnin Yogyakarta, yana sanya idanu kan ayyukan agajin da kansa. Ya roki kasashen waje da su agaza musu, ya kuma yi alkawarin samar da dala miliyan dari da bakwai domin gudanar da ayyukan sake gina yankin.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin
  Muhimmin Labari
Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton Tace Barazanar Masu Matsanancin Raayin Islama Kan Amurka Ta Fi Ta Shirin Nukiliyar Iran Da Koriya Ta Arewa

  Karin Labarai
Majalisar Dinkin Duniya Tana Bin Bahasin Zargin Laifukan Yaki Da Take Zargin Israila Da Hamas
Tarayyar Afirka Zata Ladabtar Da Duk Wadanda Suka Shirya Juyin Mulkin Soja Cikin Ko Wace Kasa A Nahiyar
Najeriya Tana Shirin Sayar da Wani Kaso  Daga Rijiyoyin Mai Dake Doron Kasa Da Cikin Teku
Shugaba Barack Obama Ya Gabatarda Jwabin Rahoton Hali Da Kasa Ke Ciki Na Farko Tun Kama Aikinsa
An Kai Hari Kan Babban Bututun daukar Mai Na Shell A Yankin Niger Delta
Malawi Ta Karbi Shugabancin Tarayyar Afirka Bayan Yunkurin Qaddafi Na Neman Tazarce Ya Faskara
Shugaban Amurka Barack Obama Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Shekara Mai Zuwa
Majalisar Ministocin Najeriya Ta Ce Shugaba Yaradua Yana Karfin Ci Gaba Da Gudanarda Aikinsa Duk Tafiyar Neman Jinya
Ana Zaman Dar Dar A Sokoto Bayan Yan Banga Sun Kashe Mutum Daya Suka Kona Gida a Unguwar Tudunwada
Alqaida Tana Gargadin Cewa Zata Ci Gaba Da Kai Hari Kan  Muradun Amurka  Idan Amurkan Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Isra'ila
Ana Baza Jita Jitar Sojoji A Najeriya Suna Shirya Juyin Mulki
Za A Yi Taron Kolin Tarayyar Afirka Makon Gobe Qaddafi Yana Shirin Tazarce A Shugabancin Kungiyar
Majalisar Dattijai Ta Najeriya Ta Yi Muhawara Kan Rashin lafiyar Shugaba Yaradua
Kotun Najeriya ta bada wa'adin tabbatar da lafiyar shugaba Yar'adua.
Kungiyar Lauyoyi Ta Najeriya Ta Nemi Kotu Ta Baiwa Mataimakin Shugaban Kasa Shugabanci Na Wucin Gadi
GWAMNATI TA SASSAUTA DOKAR HANA FITA A YAYIN DA SOJOJIN NAJERIYA KE SINTIRI A GARIN JOS
Gwamnatin Jihar Yobe Ta kafa Dokar Hana Aure Ba Tareda An Auna Jini Ba
Sojoji Suna Ci Gaba Da Sintiri A Jos Da Kewaye
SOJOJIN NAJERIYA NA KOKARIN KASHE WUTAR RIKICIN DA YA BARKE A JOS, JAHAR FILATO
Hukumomin Nigeria Sun Bada Labarin Asarar Rayuwa Ta Farko Da Aka Taba Rasawa A Sanadin Cutar Murar Aladu Ta H1n1. A Yau Ne Ma’aikatar Lafiya Ta Nigeria Ta Bada Labarin Cewa Wata Mace, 38 Mazauniya Lagos Da Ta Kamu Da Cutar, Ta Mutu A Ran 5 Ga Watan Nan Na
Jamiyyar Democrat Ta Sha  Kaye A Zaben Cike Kujerar Marigayi Edward Kennedy A Jihar Massachussetts
Mataimakin Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan Yau Ya Umurci Tura Sojoji Zuwa Jos Fadar Gwamnatin Jihar Pilato Inda Mummunan Rikicin Addini Ya Barke Tsakanin Musulmi da Kirista.
Yau Litinin Hutu Ne A Amurak Domin Karrama Gwarzon Yaki Da Wariya
Shan Taba Sigari a Afrika  Audio Clip Available
Yan Kungiyar Taliban Sun Kai Hari Kan Gine Ginen Gwamnati A Kabul
Kungiyoyin Hamayya  A Iran Suna Kira Da A Yi Zanga Zanga Ranar Bikin Yujin Juya Hali
An kafa Dokar Hana Yawo Bayan Barkewar Sabon Rikicin Addini A Jos
Kakakin Umaru Musa 'Yar'aduwa Yace Shugaban Yana Nan Da Rai
'Yan Wasan Togo Zasu Koma Gida
Bai Kamata Amurka Ta Ba Umar Farouk Abdulmutallab Lauya Ba...
An Kashe Dan Jaridar Britaniya  A Afghanistan
Shugaba Obama Ya Nemi Karin Hadin Kai Da Kasashen Musulmi Wajen Inganta Tsaron Jiragen Fasinja