Maras Hoto
Binciko Mini

 
Hukumomin Islama A Somaliya Sun Ce Sun Kwace Babban Birnin Kasar Daga Hannun Mayakan Sojojin Sa Kai

05/06/2006

Mayakan Islama na Somaliya zaune kan wata mota dauke da bindigar harbo jiragen sama da suka kwace daga hannun abokan gabarsu
Mayakan Islama na Somaliya zaune kan wata mota dauke da bindigar harbo jiragen sama da suka kwace daga hannun abokan gabarsu
Hukumomin Islama a Somaliya sun ce sun ce sun kwace babban birnin kasar a bayan fadan makonni a tsakaninsu da mayakan wasu kungiyoyin sojan sa kai.

Shugaban Kotunan Islama a Mogadishu, Sheikh Sharif Sheikh Ahmed, ya bayyana samun nasara kan kawancen sojojin sa kan a lokacin wani jawabin da ya gabatar a rediyo litinin. Ya roki mazauna birnin da su yi na'am da sabbin shugabanninsu, yana mai fadin cewa kotunan su na kwadayin maido da zaman lafiya da tsaro a birnin.

Mayakan Islama masu alaka da kotunan Shari'a sun fatattaki mayakan sa kai daga wurare da dama da suka yi tunga a Mogadishu a cikin mako gudan da ya shige. Sun samu wata babbar nasarar ranar lahadi a lokacin da suka kwace garin Balad, suka tsinke hanyar samun kayan fada na kawancen sojojin sa kai.

An ce akasarin shugabannin kungiyoyin sojan sa kai na Mogadishu sun tsere daga birnin. Mazauna birnin suka ce mayakan kungiyoyin sun fara mika makamansu ga sojojin Islama.

An kashe mutane 350 a fadan da aka gwabza har sau uku a tsakanin bangarorin biyu tun daga watan Fabrairu.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin
  Muhimmin Labari
Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton Tace Barazanar Masu Matsanancin Raayin Islama Kan Amurka Ta Fi Ta Shirin Nukiliyar Iran Da Koriya Ta Arewa

  Karin Labarai
Majalisar Dinkin Duniya Tana Bin Bahasin Zargin Laifukan Yaki Da Take Zargin Israila Da Hamas
Tarayyar Afirka Zata Ladabtar Da Duk Wadanda Suka Shirya Juyin Mulkin Soja Cikin Ko Wace Kasa A Nahiyar
Najeriya Tana Shirin Sayar da Wani Kaso  Daga Rijiyoyin Mai Dake Doron Kasa Da Cikin Teku
Shugaba Barack Obama Ya Gabatarda Jwabin Rahoton Hali Da Kasa Ke Ciki Na Farko Tun Kama Aikinsa
An Kai Hari Kan Babban Bututun daukar Mai Na Shell A Yankin Niger Delta
Malawi Ta Karbi Shugabancin Tarayyar Afirka Bayan Yunkurin Qaddafi Na Neman Tazarce Ya Faskara
Shugaban Amurka Barack Obama Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Shekara Mai Zuwa
Majalisar Ministocin Najeriya Ta Ce Shugaba Yaradua Yana Karfin Ci Gaba Da Gudanarda Aikinsa Duk Tafiyar Neman Jinya
Ana Zaman Dar Dar A Sokoto Bayan Yan Banga Sun Kashe Mutum Daya Suka Kona Gida a Unguwar Tudunwada
Alqaida Tana Gargadin Cewa Zata Ci Gaba Da Kai Hari Kan  Muradun Amurka  Idan Amurkan Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Isra'ila
Ana Baza Jita Jitar Sojoji A Najeriya Suna Shirya Juyin Mulki
Za A Yi Taron Kolin Tarayyar Afirka Makon Gobe Qaddafi Yana Shirin Tazarce A Shugabancin Kungiyar
Majalisar Dattijai Ta Najeriya Ta Yi Muhawara Kan Rashin lafiyar Shugaba Yaradua
Kotun Najeriya ta bada wa'adin tabbatar da lafiyar shugaba Yar'adua.
Kungiyar Lauyoyi Ta Najeriya Ta Nemi Kotu Ta Baiwa Mataimakin Shugaban Kasa Shugabanci Na Wucin Gadi
GWAMNATI TA SASSAUTA DOKAR HANA FITA A YAYIN DA SOJOJIN NAJERIYA KE SINTIRI A GARIN JOS
Gwamnatin Jihar Yobe Ta kafa Dokar Hana Aure Ba Tareda An Auna Jini Ba
Sojoji Suna Ci Gaba Da Sintiri A Jos Da Kewaye
SOJOJIN NAJERIYA NA KOKARIN KASHE WUTAR RIKICIN DA YA BARKE A JOS, JAHAR FILATO
Hukumomin Nigeria Sun Bada Labarin Asarar Rayuwa Ta Farko Da Aka Taba Rasawa A Sanadin Cutar Murar Aladu Ta H1n1. A Yau Ne Ma’aikatar Lafiya Ta Nigeria Ta Bada Labarin Cewa Wata Mace, 38 Mazauniya Lagos Da Ta Kamu Da Cutar, Ta Mutu A Ran 5 Ga Watan Nan Na
Jamiyyar Democrat Ta Sha  Kaye A Zaben Cike Kujerar Marigayi Edward Kennedy A Jihar Massachussetts
Mataimakin Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan Yau Ya Umurci Tura Sojoji Zuwa Jos Fadar Gwamnatin Jihar Pilato Inda Mummunan Rikicin Addini Ya Barke Tsakanin Musulmi da Kirista.
Yau Litinin Hutu Ne A Amurak Domin Karrama Gwarzon Yaki Da Wariya
Shan Taba Sigari a Afrika  Audio Clip Available
Yan Kungiyar Taliban Sun Kai Hari Kan Gine Ginen Gwamnati A Kabul
Kungiyoyin Hamayya  A Iran Suna Kira Da A Yi Zanga Zanga Ranar Bikin Yujin Juya Hali
An kafa Dokar Hana Yawo Bayan Barkewar Sabon Rikicin Addini A Jos
Kakakin Umaru Musa 'Yar'aduwa Yace Shugaban Yana Nan Da Rai
'Yan Wasan Togo Zasu Koma Gida
Bai Kamata Amurka Ta Ba Umar Farouk Abdulmutallab Lauya Ba...
An Kashe Dan Jaridar Britaniya  A Afghanistan
Shugaba Obama Ya Nemi Karin Hadin Kai Da Kasashen Musulmi Wajen Inganta Tsaron Jiragen Fasinja