Maras Hoto
Search

 
Jirgin Saman Fasinja Ya Fado Kan Mutane A Garin Goma A Kasar Kwango Ta Kinshasa

15/04/2008

faduwar Jirgi A Birnin GomaJami’ai a kasar Kwango ta Kinshasa sun ce mutane fiye da saba’in suka mutu a lokacin da wani jirgin saman fasinja ya fadi a birnin Goma dake gabashin kasar.

Jami’ai suka ce jirgin, kirar DC-9 yana dauke da mutane har 100 a lokacin da ya subuto kan wani wuri mai kasuwa ya kama da wuta jim kadan a bayan tashinsa yau talata. Suka ce mutane akalla 6 a cikin jirgin sun kubuta da rayukansu, cikinsu har da biyu daga cikin matuka jirgin.

Shaidu sunce da alamun akwai wadanda suka mutu daga cikin mutanen da jirgin ya fado a kansu.

Jami’ai suka ce jirgin na kamfanin safarar jiragen sama na Hewa Bora, ya doshi Kinshasa ne, babban birnin kasar. A makon jiya, Kungiyar Tarayyar Turai ta saka sunan kamfanin safarar jiragen saman Hewa Bora a cikin wadanda ta haramtawa jiragensu shawagi a kasashen Turai a saboda damuwa kan lafiyar jiragen nasu.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Jami'an Sojan Iran Sun Ce An fara Wata Gagarumar Rawar Daji Ta Kare Kasa Daga Hari Ta Sama

  Karin Labarai
Yau Litinin Majalisar Dinkin Duniya Zata Kaddamar Da Aiki Mafi Girma Na Rigakafin Cutar Shawara Da Ta Taba Yi
Kwallon Kafa Ya Haddasa Rikicin Diflomasiyya Tsakanin Masar Da Aljeriya
Somaliyawa 'Yan Fashi A Teku Sun Sake Kai Hari Kan Wani Jirgin Ruwan Amurka Da Suka Taba Kamawa
Yau Alhamis Za A Rantsar Da Shugaba Hamid Karzai Na Afghanistan