Maras Hoto
Search

Wakokin Aminu Ladan Abubakar, Alan Waka, Su Na Yin Kasuwa Sosai

24/05/2008
Saurari Hira Da Aminu Ala A Shirin Abari Ya Huce - Download (MP3)
Saurari Hira Da Aminu Ala A Shirin Abari Ya Huce  - (Default) (MP4)
Saurari Samfurin Wakar Daurin Gwarmai - Download (MP3)
Saurari Samfurin Wakar Daurin Gwarmai  - (Default) (MP4)

Aminudeen Ladan Abubakar (Aminu Ala)
Aminudeen Ladan Abubakar (Aminu Ala)
Ban san ko mai karanta wannan labarin ya taba jin wata waka mai suna "Daurin Gwarmai" ko kuma wata mai suna "Bara A Kufai" ba, amma na san cewa zai yi wuya a ce mai sauraro bai ji wakar nan da ake kira "Jami'a Gidan Ban Kashi" ba. Idan kuwa ka ji wannan waka, to lallai ka ji wakar Aminudeen Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da sunan Aminu Ala, ko Alan waka.

Ni dai na jima da jin wasu wakokin Aminu Ala, amma Allah da ikonSa, kwanakin baya sai ga mu a gidan telebijin na CTV a Kano, inda muka taras da Aminu Ala yana waka tare da Maryam A. Baba da Fati Nijar.

Daga bisani, mun gayyaci Aminu Ala zuwa ofishin Muryar Amurka dake Kano, inda ya tattauna da filin "A Bari Ya Huce..." dangane da salon wakokinsa da kuma yadda ya fara yin waka.

Domin jin kashin farko na tattaunarmu da Aminu Ala a filin "A Bari Ya Huce...", sai a matsa rubutun dake saman wannan labarin. Idan kuma ana son jin samfurin wakarsa ta "Daurin Gwarmai" ana iya matsa inda aka rubuta hakan shi ma a saman wannan labarin. A kuma kasance da mu cikin makonnin dake tafe yayin da zamu kawo muku cikakkiyar hirar ta mu da Alan Waka.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Jami'an Sojan Iran Sun Ce An fara Wata Gagarumar Rawar Daji Ta Kare Kasa Daga Hari Ta Sama

  Karin Labarai
Yau Litinin Majalisar Dinkin Duniya Zata Kaddamar Da Aiki Mafi Girma Na Rigakafin Cutar Shawara Da Ta Taba Yi
Kwallon Kafa Ya Haddasa Rikicin Diflomasiyya Tsakanin Masar Da Aljeriya
Somaliyawa 'Yan Fashi A Teku Sun Sake Kai Hari Kan Wani Jirgin Ruwan Amurka Da Suka Taba Kamawa
Yau Alhamis Za A Rantsar Da Shugaba Hamid Karzai Na Afghanistan