Maras Hoto
Search

A Guinea, sojoji sun harbe wani jami’in kula da kudadensu

27/05/2008

Jami’ar rundunar sojin Guinea, sunce wadansu sojoji dake bukatar a biyasu wasu kudadensu, sun harbe wani jami’in kula da kudadens, har sun ji masa ciwo. Zim_Soldiers

Jami’an sun fada a yau cewa sojojin sun raunata Manjo Korka Dioallo, a lokacin da suke wata zanga-zanga a babban birnin Guinea na Conakry. Zanga zangar ta barke ne tun a jiya Litinin, lokacin da sojojin suka rika harba harsashi a sama, a wani sansanin soji dake Conakry.

 Sojojin tsohon Prime Minista Lansana Kouyate – wanda aka kora a makon da ya gabata, yayi masu alkawarin kimanin dollar dubu daya da dari daya da suke bi bashi.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Sojoji Sun Hana Jirgin Shugaba Manuel Zelaya Na Honduras Sauka A Tegucigalpa

  Karin Labarai
A Ci Gaba Da Kokarinsa Na Yin Tazarce, Tandja Ya Rushe Kotun Tsarin Mulkin Jamhuriyar Nijar
Gwamnatin Mamadou Tandja Ta Ce Lallai Sai Ta Gudanar Da Kuri'ar Raba-Gardama
Sojoji Sun Hambarar Da Shugaban Honduras Mai Shirin Yin Tazarce
Gini Ya Rushe Ya Kashe Mutane Akalla Biyar A Lagos
Madaukakiyar Kotun Nijar Ta Soke Umurnin Da Shugaba Tandja Ya Bayar Na Shirya Zaben Raba-Gardama A Watan Agusta