Maras Hoto
Search

Barack Obama Shi Ne dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar Democrat A Amurka

04/06/2008

Barack Obama speaks to supporters in St. Paul, Minnesota, 3 Jun 2008Sanata Barack Obama ya zamo dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat a nan Amurka.

Sanata Obama, mai shekaru 46 da haihuwa, wanda  karonsa na farko ke nan da zamowa dan majalisar dattijai daga jihar Illinois, yayi magana a gaban dubban magoya bayansa cikin daren talata a birnin St. Paul a Jihar Minnesota, a cikin dakin taron da 'yan jam'iyyar Republican zasu tabbatar da John McCain a zaman dan takararsu a cikin watan Satumba.

Obama shi ne bakar fata na farko da ya zamo dan takarar shugaban kasa na wata babbar jam'iyya a tarihin Amurka. Jiya talata ya samu wakilai da suka zarce dubu biyu da dari daya da goma sha takwas da ake bukata don zamowa dan takara, a bayan da ya samu karin goyon bayan wakilai masu zaman kansu, ya kuma doke abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton a daya daga cikin jihohi biyun da suka gudanar da zabe jiya talatar.

Obama, wanda ya lashe zaben karshe na Jihar Montana, ya yabawa Uwargida Clinton a zaman jagorar da ta karfafa fata a zukatan miliyoyin jama'a.

Ita ma Clinton, wadda ta lashe zaben Jihar Dakota ta Kudu, ta yaba ma Obama a lokacin jawabin da ta yi a New York. Amma kuma ta ki yarda ta yarda cewar ta sha kaye, tana mai fadin cewa zata tuntubi magoya bayanta da shugabannin jam'iyya kafin ta yanke shawara.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Jami'an Sojan Iran Sun Ce An fara Wata Gagarumar Rawar Daji Ta Kare Kasa Daga Hari Ta Sama

  Karin Labarai
Yau Litinin Majalisar Dinkin Duniya Zata Kaddamar Da Aiki Mafi Girma Na Rigakafin Cutar Shawara Da Ta Taba Yi
Kwallon Kafa Ya Haddasa Rikicin Diflomasiyya Tsakanin Masar Da Aljeriya
Somaliyawa 'Yan Fashi A Teku Sun Sake Kai Hari Kan Wani Jirgin Ruwan Amurka Da Suka Taba Kamawa
Yau Alhamis Za A Rantsar Da Shugaba Hamid Karzai Na Afghanistan