Maras Hoto
Search

Mutane 15 Sun Mutu, 150 Sun Ji Rauni A Hare-Haren Bam A Istanbul A Kasar Turkiyya

28/07/2008

Harin Bam A IstanbulHukumomin Turkiyya sun ce mutane akalla 15 sun mutu, wasu 150 suka ji rauni a hare-haren bam guda biyu a birnin Istanbul. 

Bama-baman sun tashi 'yan mintoci kadan a tsakanin juna jiya lahadi da maraice a kan wani titi na gidajen dake da kantuna a wata unguwa mai suna Gungoren a bangaren yammacin Istanbul.

Jami'ai suka ce bam na farko ya tarwatsa wani dakin yin wayar tarho, abinda ya janyo hankalin mutanen da suka taru don kallo. daga nan ne bam na biyu mai karfin gaske ya tashi. An boye dukkan bama-baman guda biyu a kwandunan shara.

Shugaba Abdullahi Gul na Turkiyya yayi tur da harin, ya kuma bayyana wadanda suka kai shi a  matsayin 'yan ta'adda marasa imani. Hukumomi su na binciken ko su wanene suka kai harin.

A can baya, kungiyoyi da dama sun sha kai hare-hare a birnin Istanbul, ciki har da Kurdawa 'yan aware, da 'yan ra'ayin gurguzu da kuma masu kishin Islama.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Daga Mai Neman Koyan Hausa Na Zamo Babbar Mai Sha'awar Fina-Finai Da Wakokin Hausa  Audio Clip Available

  Karin Labarai
ECOWAS Ta Ce Ba Zata Amince Da Sakamakon Zaben Da Aka Yi A Nijar Ba
Yau Talata Kungiyar ECOWAS Za Ta Bayyana Dakatar Da Jamhuriyar Nijar Daga Cikin Kungiyar
Shugabannin Afirka Ta Yamma Zasu Yi Taron Koli Kan Guinea-Conakry
Ghana Ta Kai Wasan Karshe Na Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya Na Matasa A Masar