Maras Hoto
Search

A yammacin Alhamis din nan ne, dan takarar shugabancin Amurka na Jam’iyyar Democrat, Barack Obama,zaiyi na’am da tsaida shi dan takara

28/08/2008

A yammacin Alhamis din nan ne,ake sa ran dan takarar shugabancin Amurka na Jam'iyyar Democrat, Barack Obama,zaiyi na'am da tsaida shi dan takara, a jawabi da ake doki zai gabatar,wanda kuma zai kawo karshen babban taron Jam'iyyar.

 

Obama zai yi jawabi ga dubban mutane a wani dandalin wasanni mai suna "Mile High Stadium",a birnin Denver,cikin Jihar Colorado, dake yammacin Amurka.
Hillary Clinton da Barack Obama
Hillary Clinton da Barack Obama

 

Cikin sanannun  Jam'iyyar har da zasu yi jawabi ga gangamin har da  tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Al Gore,da kuma Gwamnan Jihar New Mexico,Bill Richardson, Haka kuma za a nunawa wakilai majigi kan tsohon shugaban rajin kare hakkin bil'adama, Martin Luther King,wadda yau ce cikar shekaru 45 da gabatar da fitaccen jawabin sa,da aka lakabawa suna "Ina Mafarki".
Sen. Barack Obama, (r), and Democratic vice presidential candidate, Sen. Joe Biden at the Democratic National Convention in Denver, 27 Aug 2008
Barack Obama da Joe Biden

 

Jiya Laraba da dare ne taron ya tsaida Obama da mataimakin sa Joseph Biden.Obama ne bakar fatar Amurka na farko da wata babbar Jam'iyyar siyasa ta tsayar takarar shugabancin Amurka. A jiyan tsohon shugaban Amurka Bill Clinton, ya kira Obama,mutumin da ya dace da aikin shugaban kasa.

 

 

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Jami'an Sojan Iran Sun Ce An fara Wata Gagarumar Rawar Daji Ta Kare Kasa Daga Hari Ta Sama

  Karin Labarai
Yau Litinin Majalisar Dinkin Duniya Zata Kaddamar Da Aiki Mafi Girma Na Rigakafin Cutar Shawara Da Ta Taba Yi
Kwallon Kafa Ya Haddasa Rikicin Diflomasiyya Tsakanin Masar Da Aljeriya
Somaliyawa 'Yan Fashi A Teku Sun Sake Kai Hari Kan Wani Jirgin Ruwan Amurka Da Suka Taba Kamawa
Yau Alhamis Za A Rantsar Da Shugaba Hamid Karzai Na Afghanistan