Koma Ga Shafi Mai Hoto

VOANews.com
News in 44 languages


Barack Obama ya anshi zabin da jamiyyar sa ta democrat tayi masa na zama dan takarar shugaban kasa

29/08/2008

Barack Obama ya anshi zabin da jamiyyar sa ta democrat tayi masa na zama dan takarar shugaban kasa,wanda yayi fice a tarihi, kuma ya shiga yakin neman zaben shugaban kasa na tsawon wata biyu a matsayin bakar-fatar Amurka na farko da rike tutar shugabancin  babbar jamiyya.

 

Sanata Obama da abokin takarar sa ,Sanata Joe Biden,a yau juma'a zasu tafi jahar Pennsylvania,dake arewacin Amurka akan bos da zai yawata da su manyan jahohi.

 

 

 

A daren alhamis, Obama ya bayyana gaban jama'a fiye da dubu tamanin,suna masa tafi da shewa,inda yayi alkawarin kawo canji a kasar Amurka ya kuma bayyana banbancin sa da dan hamayyar sa na jamiyyar republican,Sanata John Mccain. 

 

Muhimmin Labari
Jami'an Sojan Iran Sun Ce An fara Wata Gagarumar Rawar Daji Ta Kare Kasa Daga Hari Ta Sama

Karin Labarai
Yau Litinin Majalisar Dinkin Duniya Zata Kaddamar Da Aiki Mafi Girma Na Rigakafin Cutar Shawara Da Ta Taba Yi
Kwallon Kafa Ya Haddasa Rikicin Diflomasiyya Tsakanin Masar Da Aljeriya
Somaliyawa 'Yan Fashi A Teku Sun Sake Kai Hari Kan Wani Jirgin Ruwan Amurka Da Suka Taba Kamawa
Yau Alhamis Za A Rantsar Da Shugaba Hamid Karzai Na Afghanistan