Koma Ga Shafi Mai Hoto

VOANews.com
News in 44 languages


Ra'ayoyin Jama'a Game Da Zaben Obama

05/11/2008

Barack Obama
Ojo na titin Bugaje (titinbougajeojo@yahoo.fr) BP : 486 Zinder a Jamhuriyar Nijar, ya rubuto yana cewa, "...sashen hausa na muryar amurka ku gayama shuwagabannin siyasa  na kasarmu  Niger, Zaben kasar Amurka ya kamata ya zame musu ishara, saboda sunga yinda dan adawa zai fadi a takarar neman kuri'a ta zabe, kuma ya amince da lalle ya fadi, sannan ya kirayi magoya bayenshi da su mara ma wanda yaci domin a tafi tare dan ama kasa aiki, a gaskia wannan abu sai a Amurka. Allah yasa shuwagabanninmu wannan ishara zata zamo musu karatu a kayunansu, amin."

IBRAHIM JATAU MAI NAMA BISIJE MALUMFASHI, tare da YUSUF MAIKANO LUNGUN ALHAZAWA MALUMFASHI, sun rubuto su na cewa, "Barak Obama yau an wayi gari ALLAH yasa ka zama shugaban kasar Amurka, saura ka cika alkawuran duk da ka dauka, ka kuma yi kokarin dawo da martabar AMURKA A IDANUN DUNIYA."

Barack Obama
"Hakika  Amirkawa tabbas kunzama zakarar gwajin dafin duniya, ga shi kunyi zabenku lafiya cike da adalci, da sanin yakamata, to, Obama sai ka rike kowa hannu biyu biyu, sannan kada kamanta da irin goyon bayan da 'yan uwanka al'umar Afirka suka baka. To, yaya  babbar kwabo wato Najeriya  kinga yanda ake tafiyar da zabe cikin adalci, ba 'yan banga. ba fisge akwatun zabe, babu aiki da 'yan sanda dan su musguna ma masu kada kuri'a, to, yaya babbar kwabo Najeriya  sai kigyara tsarin zabenki  indai  kina son kici gaba da hura hanci a kasashen Afirika." Daga Sani World 7 Kusfa Zaria.(Saniworld7kusfazaria@yahoo.com)

SHUAIBU MUHAMMED RIJIYAR MAIKABI(RKB20042001@YAHOO.COM)ya rubuto ta sa takardar yana fadin cewa, "Ra'ayina shine In nuna farin cikina kan yadda "yan kasar Amuruka suka debewa kansu takaici suka tsaya suka nuna su na da "yanci sannan inyi kira ga sabon Shugaban kasar ta Amuruka wato Barack Obama da ya cika Alkawalinda yadauka yatsaya tsayin daka don maido wa kasar Amuruka martabarta."

Muhammed Usman Dandattijo Bayan NEPA, Malumfashi, Jihar Katsina, ya ce, "Assalamu alaikum ina taya Barack Obama da sauran al'umar Afrika dama duniya baki daya murnar samun nasarar cin zaben dan'uwanmu Barack Obama. Allah Ya yi masa jagora da fatan zai ba marada kunya."
Muhimmin Labari
Jami'an Sojan Iran Sun Ce An fara Wata Gagarumar Rawar Daji Ta Kare Kasa Daga Hari Ta Sama

Karin Labarai
Yau Litinin Majalisar Dinkin Duniya Zata Kaddamar Da Aiki Mafi Girma Na Rigakafin Cutar Shawara Da Ta Taba Yi
Kwallon Kafa Ya Haddasa Rikicin Diflomasiyya Tsakanin Masar Da Aljeriya
Somaliyawa 'Yan Fashi A Teku Sun Sake Kai Hari Kan Wani Jirgin Ruwan Amurka Da Suka Taba Kamawa
Yau Alhamis Za A Rantsar Da Shugaba Hamid Karzai Na Afghanistan