 |
| 'Yan tsageran Niger Delta |
Rundunar
sojojin Nijeriya ta ce wasu 'yan kasar Rasha su biyu da aka sace watanni biyu
da suka shige, sun tsere daga hannun mutanen da suke yin garkuwa da su, kuma an
ceto su.Wani kakakin sojojin, Kanar Sagir Musa, ya ce mutanen biyu sun tsere
da kafa daga sansanin da ake yin garkuwa da su. Sun shafe kwanaki biyar su na
yawo a cikin fadamu na yankin Niger Delta. Jiya alhamis wasu sojojin Nijeriya
dake yin sintiri a yankin suka tsince su, suka fito da su waje.
'Yan kasar ta
Rasha su na yin aiki ne a wata masana'antar goran ruwa dake garin Ikot Abasi
mai tashar jiragen ruwa a Jihar Akwa Ibom.
Sace mutane da kai hare-hare sun
zamo ruwan dare a yankin kudancin Nijeriya mai arzikin fetur. Har yanzu
Nijeriya ce kasar da ta fi sayarwa da kasashen waje man fetur a nahiyar Afirka
duk da cewa yawan man da take hakowa ya ragu da kashi ashirin cikin 100 a
shekaru ukun da suka shige a saboda sace-sacen mutane da hare-haren da ake
kaiwa kan cibiyoyin mai na yankin.