Dakarun Tsaron Nijar Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zangar Kin Jinin Tazarce A Dosso
Marubuci Ibrahim Alfa Ahmed 02/06/2009
Shugaba Mamadou Tandja na Nijar
Dakarun
tsaro a Jamhuriyar Nijar sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa 'yan
zanga-zangar da suke yin Allah wadarai da yunkurin shugaba Mamadou Tandja na
sauya tsarin mulkin kasar domin ya nemi wa'adi na uku a kan karagar mulki.
Shaidu sun ce dakarun sun kutsa don tarwatsa taro a bayan da masu zanga-zanga
suka lalata gine-ginen gwamnati da motoci jiya litinin a garin Dosso, mai
tazarar kimanin kilomita 140 a kudu maso gabas da Yamai, babban birnin kasar.
A bisa tanadin da
tsarin mulkin Nijar yayi, shugaba Tandja zai sauka daga kan mulki a karshen
wa'adinsa na biyu a watan Disamba, amma kuma yace yana son a yi kuri'ar
raba-gardama domin a kawar da wannan ka'idar da ta tanadi yawan wa'adin shekaru
biyar-biyar da shugaba zai yi a kan mulki.
A ranar jumma'a kotu mafi girma ta
Jamhuriyar Nijar ta yanke hukumcin cewa gudanar da irin wannan kuri'ar
raba-gardama haramun ne, amma shugaba Tandja yace zai ci gaba da wannan shiri
nasa na yin tazarce. Haka kuma, shugaban na Nijar ya rushe majalisar dokoki,
yana mai fadin cewa ana bukatar yin hakan don tabbatar da kwanciyar hankali a
kasar mai arzijkin karfen Uranium.
A bayan wadanda suka yi zanga-zanga jiya a
Dosso ma, wasu gungun jam'iyyun siyasa da kungiyoyin kwadago sun hada karfi
wuri guda domin su yaki kokarin shugaban da masu taya shi buga gangar tazarce.
Da alamun ita kanta jam'iyyar MNSD ta shugaba Tandja kanta yana rabe game da
wannan batun, inda wasu 'ya'yan MNSD suke goyon bayan tsohon firayim minista Hama
Amadou, mutumin da aka jima ana ganin zai yi takarar shugaban kasa.