VOANews.com

 
Labarai Cikin Harsuna 45
Kamfanin Man Shell Zai Biya Diyyar Dala Miliyan Goma Sha Biyar Ga Wasu 'Yan Nijeriya

09/06/2009

Shell
Shell
Kamfanin man fetur na Shell      ya yarda zai biya dala miliyan 15 da dubu dari biyar ga wadanda suka kai      kararsa bisa zargin hannu a keta hakkin bil Adama a Nijeriya, domin su      janye wannan karar.

Wannan yarjejeniyar biyan kudin da aka cimma jiya      litinin a New York ita ta kawo karshen shari’ar da aka shafe shekaru fiye      da gom ana gwabzawa a tsakanin kamfanin Shell da ‘yan’uwan masu      zanga-zangar da tsohuwar gwamnatin mulkin soja ta Nijeriya ta yankewa      hukumcin kisa a 1995.

Mutanen sun hada da marubucin wakoki Ken Saro-Wiwa,      wanda ya jagoranci zanga-zangar rashin amincewa da zaman kamfanin Shell a      yankin Niger Delta. Masu zanga-zangar sun ce kamfanin Shell ya gurbata      yanayin yankin ya kuma keta hakkin ‘yan kabilar Ogoni.

Haka kuma sun zargi      kamfanin da laifin hada baki da gwamnati wajen hukumta wadanda suka soki      lamirin kamfanin. Kamfanin Shell dai ya ce shi bai aikata wani laifi ba,      amma yace ya yarda mutanen sun sha wahala. 


E-mail This Article Aika Labarin Nan ma Wani Ta E-Mail
Print This Article Shafi Mai Saukin Bugawa
  Muhimmin Labari
Kwallon Kafa Ya Haddasa Rikicin Diflomasiyya Tsakanin Masar Da Aljeriya

  Karin Labarai
Somaliyawa 'Yan Fashi A Teku Sun Sake Kai Hari Kan Wani Jirgin Ruwan Amurka Da Suka Taba Kamawa
Yau Alhamis Za A Rantsar Da Shugaba Hamid Karzai Na Afghanistan
Switzerland Ta Doke Nijeriya A Wasan Karshe Na Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya Na Samari
Dan Kunar-Bakin-Wake Ya Kai Farmaki Kan Hukumar Leken Asirin Pakistan