VOANews.com

 
Labarai Cikin Harsuna 45
Madaukakiyar Kotun Nijar Ta Soke Umurnin Da Shugaba Tandja Ya Bayar Na Shirya Zaben Raba-Gardama A Watan Agusta

13/06/2009

Shugaba Mamadou Tandja na Nijar
Shugaba Mamadou Tandja na Nijar
Madaukakiyar kotun Jamhuriyar Nijar ta yanke hukumcin cewa shirin shugaba Mamadou Tandja na gudanar da kuri'ar raba-gardama domin kara tsawon wa'adinsa a kan mulki ya saba ma doka, saboda haka haramun ne.

Jiya jumma'a kotun tsarin mulki ta Jamhuriyar Nijar ta ce ta soke umurnin da shugaba Tandja ya bayar ranar 5 ga watan Yuni a kan a gudanar da kuri'ar raba-gardamar a cikin watan Agusta.

Kotun ta ce umurnin da shugaban ya bayar ya saba ma tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar. Tsarin mulkin ya kayyade cewa shugaban kasa zai iya yin wa'adi biyu ne kawai na shekaru biyar-biyar a jere kan mulki.

Shugaba Tandja ya ce yana son karin lokaci a kan kujerar shugaban kasar domin ya kashe wutar tawayen da Abzinawa suke yi, da fadada ayyukan samar da kayan bukatu da kuma ba da karin iko ga kujerar shugaban kasa.

Wannan shiri nasa ya hassala 'yan hamayyar siyasa da shugabannin kwadago na Jamhuriyar Nijar. Haka kuma, hukumomin kasashen Afirka da kuma gwamnatin Amurka sun fito da kakkausar harshe su na sukar lamirin wannan shirin yin Tazarce.

Wa'adin shugaba Tandja a kan mulki zai kare a watan Disamba, amma ya sha nanata cewa ya kamata a canja wannan.

A can baya, kotun tsarin mulkin ta ayyana cewa shirin Tazarcen na shugaba Tandja ya keta doka. A bayan wannan ne sai shugaban ya rushe majalisar dokoki. Sai dai kuma hukumcin da Kotun Tsarin Mulkin  ta yanke a jiya jumma'a, hukumci ne da tsarin mulkin kasar ya bukaci cewa tilas a yi aiki da shi.


E-mail This Article Aika Labarin Nan ma Wani Ta E-Mail
Print This Article Shafi Mai Saukin Bugawa
  Muhimmin Labari
Daga Mai Neman Koyan Hausa Na Zamo Babbar Mai Sha'awar Fina-Finai Da Wakokin Hausa  Audio Clip Available

  Karin Labarai
ECOWAS Ta Ce Ba Zata Amince Da Sakamakon Zaben Da Aka Yi A Nijar Ba
Yau Talata Kungiyar ECOWAS Za Ta Bayyana Dakatar Da Jamhuriyar Nijar Daga Cikin Kungiyar
Shugabannin Afirka Ta Yamma Zasu Yi Taron Koli Kan Guinea-Conakry
Ghana Ta Kai Wasan Karshe Na Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya Na Matasa A Masar