![[insert caption here] [insert caption here]](/hausa/Archive/images/rtv_asia_17nov01_pak_ramadan_mosque_150.jpg) |
Musulmi Su Na sallah
|
Akasarin
al'ummar Musulmi a fadin duniya su na shirye-shiryen fara azumin watan Ramadan,
wata mai tsarki a Musulunci, daga asabar. Addinin Musulunci yana amfani da bayyanar wata
wajen tsaida ranar farko ko ta karshen wata.Shugabannin addinin Musulunci a
fadin duniya sun ce ba a samu ganin wata ba a ranar alhamis, a saboda haka aka
tsaida jumma'a ta zamo ranar karshe ta watan Sha'aban.
Musulmi a kasashe
kamar Nijeriya, Aljeriya, masar, Indonesiya, Iraqi, Sudan, Syria, Somaliya,
kasashen yankin Gulf da yankunan Falasdinawa da ma nan Amurka duk zasu tashi da
azumi asabar idan Allah Ya kai mu.
A tsawon watan Ramadan, Musulmi su na
gujewa cin abinci ko shan ruwa ko jima'i da wasu abubuwan da dama daga ketowar
alfijir har zuwa faduwar rana.