Shugaba Hamidu Karzai da Babban Abokin Hamayyarsa Duk Sun Fito Su Na Ikirarin Samun Nasara
Marubuci Ibrahim Alfa Ahmed 21/08/2009
Mata su na layin jefa kuri'a a Afghanistan
Kwamitocin
yakin neman zaben manyan 'yan takara biyu a zaben shugaban kasa na Afghanistan
duk sun fito su na ikirarin samun nasara. Amma hukumar zabe ta kasar ta ce har
yanzu babu tabbas a kan ko wanene ya lashe zaben na alhamis.
Jami'an yakin
neman zaben shugaba Hamidu Karzai sun ce ratar da ya bayar tana da yawan da ba
za a bukaci gudanar da zagaye na biyu na zaben fitar da gwani ba. Wani kakakin
babban abokin hamayyar Karzai, tsohon ministan harkokin waje Abdullah Abdullah,
shi kuma yayi ikirarin cewa dan takararsu ne ke da rinjaye.
Amma kuma, sakatare
janar na hukumar zabe mai zaman kanta, Daoud Ali Najafi, yace ba a kidaya
dukkan kuri'un da aka kada ba, saboda haka babu wanda zai iya ikirarin samun
nasara. An kammala kidaya akasarin kuri'un, amma sai a yanzu ne ake kai su
Kabul, babban birnin kasar inda za a tattara a lissafa.
Sai a farkon mako mai
zuwa ne ake sa ran za a fara samun sakamakon zaben.
Mazan ma ba a barsu a baya ba...
A muhimmin bayani na farko
da aka samu daga 'yan kallo a zaben, Cibiyar Republican ta Amurka ta fada a yau
jumma'a cewa an kamanta gaskiya a wannan zabe. Amma kuma jagoran 'yan kallon
cibiyar da aka tura Afghanistan, Richard Williamson, yace akwai manyan
matsalolin da aka fuskanta.
Yace rashin tsaro sosai ya rage yawan mutanen da
suka fito, kuma an samu rahotanni masu tushe na sayarda katunan rajistar jefa
kuri'a. Har ila yau Williamson yace an samu matsala da tawadar nan da ake
amfani da ita don tabbatar da cewa mutum bai jefa kuri'a fiye da sau daya ba.
Duk da barazanar da 'yan Taliban suka yi ta kai hare-hare, 'yan Afghanistan da
yawa sun fito suka kada kuri'u a zaben shugaban kasa na biyu a
kasar. An kashe mutane akalla 26 a tashin hankali a Kabul da Kandahar da wasu
manyan biranen kasar.