 |
Harba makamin Shahab-3 Ranar 27 Satumba 2009
|
Iran
ta ce ta samu nasarar gwajin biyu daga cikin makamanta masu linzami da suka fi
cin dogon zango, wadanda masu fashin bakin harkokin tsaro suka ce su na iya kai
wa kan Isra’ila ko kudancin Turai.Jiya litinin, gidan telebijin na Iran ya
nuna tashin makami mai linzami samfurin Shahab na Uku cikin kura a wata hamada.
An yi imanin cewa wannan makami mai linzami da ake harbawa daga doron kasa zuwa
doron kasa yana iya cin kilomita dubu 2.
Wakilan Britaniya da Faransa da Jamus
da kuma Tarayyar Turai sun bayyana damuwa kan wannan gwajin. Fadar shugaban
Amurka ta White House ta bayyana gwajin a zaman "tsokana" ta kuma bukaci
hukumomin Iran da su kyale sufetoci su shiga cikin sabuwar masana’antar tace
man nukiliya ta Iran da aka gano ba tare da tsangwama ba.
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya bayyana gwaje-gwajen a zaman abin "damuwa." Kamfanonin dillancin labarai na Rasha sun ambace shi yana kira ga Iran da ta bayar da cikakken hadin kai ga sufetocin nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya.
Amurka da sauran manyan kasashen duniya zasu matsa lamba kan kasar Iran da ta bayyana dukkan ayyukan nukiliyar da ta ke gudanarwa a wajen ganawar da zasu yi da ita ranar alhamis a birnin Geneva.