Ghana Ta Kai Wasan Karshe Na Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya Na Matasa A Masar
Marubuci Ibrahim Alfa Ahmed 14/10/2009
Wani wasa tsakanin Ghana da Brazil
‘Yan
kwallon kafar matasa na kasar Ghana sun yi waje-rod da ‘yan wasan kasar Hungary
da ci 3-2 domin kaiwa ga wasan karshe na cin kofin duniyar matasa ‘yan kasa da
shekara 20 a Masar.
Abeiku Quansah shi ne ya jefa kwallo na uku da ya ba Ghana
nasara a minti na 81 da fara wasa. Dominic Adiyiah, wanda shine ya fi kowa jefa
kwallaye a wannan gasa baki daya, ya jefa kwallaye har guda biyu tun kafin a
tafi hutun rabin lokaci.
Wannan shine karo na uku da Ghana take kaiwa wasan
karshe a wannan gasa ta ‘yan kasa da shekara 20. Ghana dai zata yi kokarin
lashe wannan kofin a karon farko, domin a bayyanar da ta yi a wasannin karshe a
2001, ta sha kashi a hannun Ajantina, a 1993 kuma Brazil ce ta doke ta.
A
wannan karo na ukun ma, Ghana zata kara ne da kasar Brazil, wadda ta cire kasar
Costa Rica da ci daya mai ban haushi.