 |
TWani taron kolin ECOWAS a Ouagadougou a 2007
|
Shugabannin
kasashen Afirka ta Yamma sun yarda zasu yi taron koli cikin wannan makon domin
tattauna tankiyar siyasar da ta ke akwai a kasar Guinea-Conakry. Za a yi wannan
taron kolin ranar asabar a Abuja, babban birnin Nijeriya, a ranar da ita ma
Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta shirya ganawa domin tattauna yiwuwar
kafa takunkumi a kan gwamnatin mulkin soja ta kasar Guinea.
An yi Allah wadarai
da gwamnatin ta mulkin sojan Guinea, hagu da dama, a saboda wutar da sojojinta
suka bude a kan masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a ranar 28 ga watan
Satumba.
Majalisar Dinkin Duniya, MDD, da wata kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasar sun ce an kashe
mutane dari da hamsin da bakwai. Gwamnati Guinea ta ce mutane hamsin da bakwai na kai kawai aka kashe, ta
kuma ce akasarinsu an tattake su ne suka mutu lokacin da mutane ke ribibin fita
daga filin wasan Conakry, babban birnin kasar.
Jiya talata, titunan babban birnin
sun kasance wayam a rana ta biyu ta yajin aikin gidan kowa da shi da aka shirya domin
tunawa da wadanda aka kashe. Kungiyoyin kwadago ne suka shirya wannan yajin
aiki na kwana biyu domin jimamin wadanda suka mutu.