![[insert caption here] [insert caption here]](/hausa/Archive/images/ap_SAUuDI_HAJJ_150.jpg) |
Aikin Hajji
|
Ruwan
sama kamar da bakin kwarya da kuma ambaliyar da ya haddasa, sun kashe mutane akalla 11 jiya
laraba a Sa’udiyya, a yayin da miliyoyin Musulmi suka shiga haramar fara aikin
Hajjin bana.
Ruwan da aka shafe tsawon rana jiya laraba ana tabkawa, ya kawo
ambaliya a kan tituna, ya haddasa cunkoson ababen hawa, ya katse wutar
lantarki, ya kuma sa mutane suka kasa fita daga cikin gidajensu. Wasu
mahajjatan sun kasa samun hanyar wucewa a yayin da suka doshi birni mai Tsarki
na Makka daga birnin Jeddah.
Mutanen da suka samu isa wurare masu tsarki ba su
kai na shekarun baya ba ya zuwa jiya larabar.
A jiyan, mahajjata cikin harami
sun yi dawafi a dakin Ka’abah mai tsarki. Ana sa ran mahajjata miliyan biyu da
rabi ne zasu yi aikin Hajjin bana, yayin da hukumomi suke aiki ka’in da na’in
don kawar da damuwa game da cutar murar aladu da kuma tsaron lafiyar
mahajjatan.
Shugaba Barack Obama na Amurka ya bada sanarwa jiya laraba, yana
mika sako na fatar alheri ga Musulmin dake aikin Hajji a Sa’udiyya tare da taya
illahirin Musulmi na duniya murnar Sallar layya da za a yi kwana guda bayan
hawan Arafat.
Shi ma babban kwamandan sojojin Amurka da na NATO a Afghanistan,
Janar Stanley McChrystal, ya aike da sakon Barka da Sllah ga Musulmi ya kuma yi
kira ga al’ummar Afghanistan da su yi aiki da akidojin addinin Musulunci kamar
gaskiya, da halin kwarai da adalci da kuma ‘yanci don sake gina kasar
Afghanistan.