 |
| Shugaba Barack Obama |
Fadar
White House ta ce shugaba Barack Obama zai bayyana sabuwar manufarsa kan
Afghanistan ranar talata da daddare, a cikin wani jawabin da zai yi ga kasa
daga babbar makarantar horas da sojoji ta Amurka dake West Point a Jihar New
York.
Jiya laraba kakakin fadar ta White House, Robert Gibbs, ya bada sanarwar
shirin na shugaba Obama. Gibbs yace sojojin Amurka sun shafe shekaru takwas
yanzu haka a kasar Afghanistan, ya kuma ce Amurka ba zata zauna a can
Afghanistan na wasu karin shekaru 8 ko 9 ba.
Wannan sanarwa ta biyo bayan
makonnin da shugaban ya shafe yana ganawa da manyan masu ba shi shawara game da
tsaron kasa a kan hanyoyin da suka kamata a bi don takalar batun Afghanistan.
Kafofin labarai sun ba da rahotannin cewa a bisa dukkan alamu, Mr. Obama zai
amince da wani shirin da ya tanadi tura karin sojoji akalla dubu 30 na Amurka zuwa can. Mr. Obama ya lashi takobin karasa aikin da aka fara a Afghanistan. A yanzu
haka akwai sojojin Amurka dubu 68 a Afghanistan din.