 |
Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya a Somaliya
|
Wakilin Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka, KTKA, a Somaliya yace rabon da a biya sojojin kiyaye zaman lafiya dake kasar
albashinsu tun watan Mayu, watau fiye da watanni shida da suka shige.Nicolas
Bwakira ya fada jiya laraba cewa kasashe masu bayar da agaji sun bayar da wani
gutsuri ne kawai na kudaden da suka yi alkawarin bayarwa wata da watannin da
suka shige don karfafa tsaro a Somaliya. A watan Afrilu, masu bayar da agaji
sun yi alkawarin bayar da kudi fiye da dala miliyan 250 domin kara yawan
sojojin KTKA da na gwamnatin Somaliya a cikin kasar.
Bwakira yace rashin bayar
da kudin yana gurgunta aikin Tarayyar Afirka a Somaliya, yayin da guiwoyin
sojojin kiyaye zaman lafiyar da na gwamnatin Somaliya duk sun yi sanyi.
Akwai
sojojin KTKA su kimanin dubu 4 daga Uganda da Burundi su na taimakawa wajen
kare gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya daga hare-haren 'yan tawayen dake son
kafa jamhuriyar Islama. Sojojin kiyaye zaman lafiyar akasari su na gadin
muhimman wurare ne kamar filin jirgin saman Mogadishu, da tashar jiragen ruwa
da kuma fadar shugaban kasa.