VOANews.com

 
Labarai Cikin Harsuna 45
Shugaba Barack Obama Ya Gabatarda Jwabin Rahoton Hali Da Kasa Ke Ciki Na Farko Tun Kama Aikinsa

28/01/2010

  

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga majalisun dokokin Amurka su yi aiki kan muhimman bukatun cikin gida da gwamnatinsa ta sa gaba,kamar kiwon lafiya da kuma tattalin arziki, a jAwabinsa na farko da ake kira state of the Union, a turance, ko rahoton hali da kasa take ciki na shekara shekara da ya gabatar.

Da yake magana a zaman hadin guiwar majalisar wakilai  data dattijai a daren jiya laraba,Mr. Obama ya yi kiraga majalisa ba tareda bata lokaci ba ta tura masa dokar samar da aikin yi. Saboda haka yace,  "batun aiki shine burinmu na farko cikin wan nan shekara ta 2010,shi yasa nake kira a wan daren, na kafa sabuwar dokar samar da ayyukan yi". Haka kuma yayi kira da aza sabon harsashi na ci gaban tattalin arziki dake hangen gaba,saboda tinkarar matsalolin tattalin arziki da Amurkawa suke fuskanta.

Mr. Obama ya lashi takobin ci gaba da yaki na garambawul ga kiwon lafiya,yana mai cewa idan majalisa bata amince da kudurin ba,kudin Inshora zai kara tashi,kuma gibin kasafin kudi zai kara haurawa.

Sabon Gwamnan Virginia, Bob McDonnell, dan republican shi ne ya  maida martani a madadin jam’iyyarsa ta Republican. Yace gwamnatin tarayya tana neman daukan abinda ya fi karfinta,sakamakon haka zata baral’uma mai zuwa da dumbin bashi.

 

 

 


E-mail This Article Aika Labarin Nan ma Wani Ta E-Mail
Print This Article Shafi Mai Saukin Bugawa
  Muhimmin Labari
Yau Ce Ranar Badar A Majalisar Wakilan Amurka Kan Dokar Grambawul Ga Tsarin Inshoran Kiwon Lafiya A Amurka

  Karin Labarai
Nahiyar Afirka ta yi taron dangi don yaki da barkewar cutar Polio
    Fiya da mutane miliyan 9 ne ke kamuwa da cutar tarin fuka (TB) duk    shekara, inda miliyan 1.7 daga cikinsu kan mutu 
Nijeriya Ta Janye Jakadanta Daga Libya
Goodluck Jonathan Ya Saukar Da Dukkan Ministoci
An Yi Sabon Rikici A Jihar Filato
Aljeriya Ta Cimma Yarjejeniya Da Wasu Kasashen Afirka Shida Wajen Yaki Da Taaddanci