blank

Inside VOA | Tuntube Mu

Tafi Da Gidanka

Muryar Amurka (VOA) tana samar muku da labarai, kyauta, da dumi-duminsu ta wayoyinku na salula!

Idan wayarkab tana iya kama Internet, to jeka m.voanews.com/hausa domin samun labaran Hausa na VOA!

Karin Bayanai


Tambaya: Ta yaya zan iya kama VOA a wayata?

Domin samun labaran VOA da Hausa, sai a buga m.voanews.com/hausa a jikin falle (browser) da ake amfani da shi wajen bude wani shafi na Internet a jikin wayar hannu ko salula.
Za ku iya samun labaran Hausa na VOA kyauta daga duk wata waya ko na’urar hannu muddin dai tana iya kama Internet.

↑ Koma saman shafi


Tambaya: Wasu abubuwa VOA ke samarwa ta wayar salula?

A dandalinmu na m.voanews.com/hausa zaka iya karantawa ko sauraron manyan labarai na wannan rana cikin harshen Hausa, daga kowace kusurwa ta duniya. Zaka iya sauraron labarai ko rahotanninmu na minti biyu, da dumi-duminsu, sau uku a rana. ou can read or listen to the day's top stories from around the world in Hausa.

↑ Koma saman shafi


Tambaya: VOA tana cajin wani kudi ne don samun labaranta ta waya?

VOA ba ta cajin ko sisin kwabo don shiga dandalinta ta wayar salula. Sai dai a lura cewa kamfanin wayar salula su na iya cajin wani abu na kama Internet a waya. Ku tuntubi kamfanin wayarku don neman bayanin kama Internet daga gare su.

↑ Koma saman shafi


Tambaya: Na shiga dandalin VOA ta waya, amma na kasa karanta komai. Yaya zan yi?

An yi gwajin dukkan abubuwan da VOA ke sanyawa a dandalinta na wayar salula domin tabbatar da cewa za a iya gani a wayoyi dabam-dabam. Watakila, wasu tsoffin wayoyin salula ba zasu iya nuna abubuwan Internet na yanzu ba, abinda ya sa za a iya ganin matsala wajen karanta abubuwan dake wannan dandali.
Idan ana da wata tambaya ko kuma yin sharhi game da wannan dandali namu na wayar salula, ana iya rubuto mana sako zuwa ga mobile@voanews.com.
Idan kana fuskantar matsala wajen karanta labarai a wani harshe, to sai a fada mana sunan harshen. Idan kuma kana iya karanta wasu abubuwan da aka rubuta da wannan harshe a wasu kafofin dabam, to a fada mana kafofin da ake iya karantawa.
Kada a manta, a fada mana sunan kasar da kake, da sunan kamfanin wayar salularka, da irin wayar da kake amfani da ita, har ma da lambar model dinta.

↑ Koma saman shafi