Akalla mutane 74 ne ake zargin dakarun Syria suka kashe ciki har da ‘yan jarida daga kasashen yammacin duniya biyu a fadin kasar a wunin jiya laraba, musamman a birnin Homs babbar tungar ‘yan hamayya, sakamakon barin bam babu  kakkautawa da dakarun suka yi.

Gwamnatin Faransa ta bayyana ‘yan jarida biyu da aka kashe a Homs, da  cewa sune Marie Colvin, ba Amurkiya  fitacciyar wakili a fagen daga dake aiki da jaridar Sunday Times ta Ingila da kuma wani dan Faransa  mai daukan hotuna Remi Ochlik.

‘Yan gwagwarmaya sunce ‘yan jarida masu yawa dake aiki a wata cibiyar ‘yan jarida  ta wucin gadi sun jikkata a gundumar Baba Amr dake hanun ‘yan tawaye, kuma suka ce da gangan aka auna hari kan cibiyar.

PM Ingila David Cameron yayi ta’ziyya  da jinjinawa ga Colvin.

Gwamnatin Syria ta bada sanarwa wacce a ciki tace  bata da  labarin cewa ‘yan jaridan suna cikin kasar. Daga nan tayi kira ga duk wani mai neman labarai dake cikin kasar ba bisa ka’ida  ba ya dauki matakin dai-daiata zamansa  cikin kasar.