Jiya Jumma’a  a Havana,shugaban juyin juya hali a Cuba Fidel Castro, ya gargadi ma’aikatan difilomasiyyar kasar su  yi hattara, domin akwai yi yuwar a  gwabza yaki da makaman Nukiliya. Castro wanda ya ziyarci Ma’aikatar harkokin wajen  Cuba a  Havana,  ya  yi hasashen za’a gwabza yakin da makaman kare dangin, idan Amurka da Isra’ila suka ci gaba da matsin lamba a kakabawa Iran takunkumi kan shirin Nukiliyarta.

Haka kuma ya  yi hasashen Amurka za  ta kai wa KTA hari.
Tsohon shugaban kasan ya amsa  tambayoyi fiyeda  sa’a daya da  rabi  daga jakadu.

Tun watan Yuli a 2006 ne aka daina ganin Castro a bainar jama’a,bayan an yi masa tiyata a  hanji,sakamakon haka ya mika iko ga kanin sa Raul Castro, wadda ahalin yanzu shine shugaban kasa.