Rahoto Na Musamman Kan Kalubalen Tsaro A Najeriya
Matakan tsaro da aka dauka na farko domin shawo kan hare haren kungiyar Boko Haram a Maiduguri
Kungiyar Boko Haram dake tada kayar baya a arewacin Najeriya wadda ta yi sanadin asarar daruruwan rayuka da jikkata da dama da kuma asarar miliyoyin kaddarori, ta fara zafafa hare harenta ne a jihar Borno, jihar ta ta kasance cibiyar kungiyar bayan kashe shugabanta Mohammed Yusuf bayan jami’an tsaro sun kama shi. A wannan rahoton na musamman, Grace Alheri Abdu ta yi nazarin matakan da jami’an tsaro suka fara dauka a yunkurinta na shawo kan kungiyar sai dai kawo yanzu, hakarsu bata cimma ruwa ba.
Part 3: Matakan tsaro da aka dauka na farko domin shawo kan hare haren kungiyar Boko Haram a Maiduguri- 21 Fabrairu 2012 (11:35) Right click (Control click for Mac) and choose Save Link/Target As
Download: MP3

