Babbar hukumar kula da harkokin adddinin Islama a Indonisiya ta  ce da jumawa musulmin kasar basa fuskantar alkibla dai dai.

Majalisar malaman kasar, litinin din nan  ce, ta  fito fili t ace ta yi kuskure tun  cikin watan Maris, da  ta auna alkiblar  ta yammacin kasar.

Shugaban majalisar malaman Ma’aruf Amin, yace bayan tuntubar masana taswirar Duniya, da malaman  taurari, hakan  ya nuna cewa musulman Indonisiya, kudancin Somalia da Kenya suke fuskanta idan suka zo Sallah, ba makka  ba,wanda yake kilomita dubu daya dari shida daga can arewacin kassar.

Amin ya bukaci musulmin su dan su karkato arewaci, idan za  su yi sallah. Yace wan nan kuskure ba yana nufin sallarsu ba  ta karbu  ba, yace Allah yasan ‘yan Adam suna kuskure. Koda shike dai Indonisiya ba bin tafarkin gama  mulki da  harkar addini, ita ce kasa da tafi ko wacce yawan musulmi a Duniya,kusan milyan 243.