Rasha ta bayyana rashin amincewarta kan daftarin kudurin hadin guiwa  da turai da kuma kasashen larabawa suka wallafa,  aka rabawa wakilan kwamitin sulhu ranar  jumma’a. Duk da haka Moscow tace  a shirye take a yi shawarwari.

Jakadan Rasha  a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin, yace daftarin baiyi la’akari da sassa da  Rasha ko kusa  ba  zata amince  dasu ba, kamar takunkumin hana sayarwa Syria makamai.

Daftarin ya goyi bayan kduurind a kungiyar hada  kan kasashen larabawa ta zartasa wadda ya nemi shugaba Assad ya mika iko ga mataimakinsa a kafa gwamnatin hada kan kasa, san a shirya yin zabe.

Ana sa ran ranar talata mai zuwa babban sakatern kungiyar kasashen larabawan Nabil AlAraby, da PM Qatar zasu yi bayani ga wakilan kwamitin sulhu kan ayyukan wakilan ayyukan sa ido da  kungiyar ta tura Syria wadda suka yi aiki na tsawon wata daya a Syria kuma suka fuskanci matsaloli  yayin wan nan aiki.

Haka kuma ana ji cikin makon mai zuwa  ne kungkyar zata gabatar  wa kwamitin sulhu wan nan kuduri data zartas a hukumance, daga nan ne ake sa ran kwamitin sulhun zai kada kuri’a akai ba da jumawa ba bayan haka.

Ahalinda ake ciki kuma tarzoma sai kar a tsanani take a Syrian a jiya jumma’a , har kaa bada rahoton an kashe akalla mutane 70 a baya bayan nan.