A yau laraba kasar Sin ta bayar da takardar
gargadi game da cutar murar tsuntsaye, bayan da cutar ta kashe wata mace,
sannan ta rufe kasuwannin sayar da kaji domin yi musu feshin kashe kwayoyin
cutar a wani lardin dake kusa da birnin Beijing. Wannan mace ita ce ta farko da
cutar ta kashe a kasar Sin a cikin shekara guda.
Matar, mai shekaru 19 da haihuwa, ta
mutu a sanadin kwayar cutar murar tsuntsaye ta H5N1, a bayan da ta taba kaji a
lardin Hebei. Wannan shi ya kawo adadin mutanen da cutar ta kashe a kasar Sin
zuwa 21 ya zuwa yanzu.
A garin Yanjiao inda matar ta sayi
agwagi a lardin Hebei, an rufe kasuwannin sayar da dabbobi dangin tsuntsaye,
aka dakatar da sayar da su yayin da ma’aikata sanye da fararen kaya, kuma da
fuska a rufe, suka bi su na fesa maganin kashe wkayoyin cutar.
Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, ta
ce da alamu wuri guda kawai wannan abu ya shafa. Cikin wata sanarwar da ta
bayar, hukumar ta ce, “babu shakka muna damuwa kwarai a duk lokacin da wannan
kwayar cutar murar tsuntsaye ta kama wani mutum, amma kuma wannan lamari da ya
faru (a Hebei) lokacin yankawa da kokarin dafa agwagwa, bai canja hasashen da
muka yi tun farko kan wannan cuta ba.”
Kwayar cutar murar tsuntsaye ta fi
yaduwa lokacin sanyi a tsakanin watannin Oktoba zuwa Maris, koda yake bullar
kwayar cutar a kasar Sin ta nuna alamun sako-sako wajen kula da bullarta a
jikin kaji ko agwagi. Kakakin ma’aikatar kiown lafiya ta kasar Sin, Mao Qunan,
ya fadawa kafofin labarai na kasar cewa gwamnati zata kara kaimin sanya idanu.
Kamfanin dillancin labaran kasar Sin na
Xinhua, ya ce a Beijing, babban birnin kasar, ma’aikata sun yadu domin bincike
a kasuwannin sayar da dabbobi dangin kaji da gidajen yanka su a bayan da
gwamnati ta bayar da takardar kashedin bullar cutar.

