Hukumar
Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce annobar cutar da ta bulla a
Kwango-ta-Kinshasa ba ta yadu zuwa kasar Angola, makwabciyarta ba.
Darektan
yanki na hukumar WHO a Afirka, Luis Gomes Sambo, ya fadawa ‘yan jarida a birnin
Luanda cewar babu wani dalili na tada hankali, kuma babu wata shaida da aka
gani cewar kwayar cutar Ebola mai saurin yin kisa ta tsallaka bakin iyaka ta
shiga Angola.
Mr.
Sambo yayi magana da ‘yan jarida ne a bayan da ya gana da shugaba Jose Eduardo
Dos Santos na Angola, inda yayi masa bayanin barkewar annobar cutar Ebola da ta
kashe mutane akalla 14 ya zuwa yanzu a yankin kudu maso yammacin Kwango.
Akalla
larduna biyu na kasar Angola sun rufe bakin iyakokinsu da kasar
Kwango-ta-Kinshasa domin kawar da yiwuwar yaduwar wannan cuta daga makwabciyar
ta su.
Cutar
zazzabin Ebola mai haddasa yoyon jini daga sassan jikin bil Adama, tana daya
daga cikin cututtukan da suka fi yin kisa a duniya, inda take kashe mutane
hamsin zuwa mutane casa’in daga cikin mutane 100 da suka kamu da ita.
Ana daukar wannan cuta daga jini ko kuma ruwan jikin mai dauke da cutar, kuma ta kan haddasa jini yayi ta zuba ba tsayawa daga idanu, kunnuwa, baki da wasu sassan jikin da

