A
yayin da akasarin masana kimiyya da dama suka dukufa kan neman hanyar warkar da
cutar kanjamau ko SIDA, wasu daga cikinsu sun maida hankali ne ga samo hanyoyi
mafiya nagarta na dakile yaduwar kwayar halittar dake haddasa wannan cuta,
watau HIV. An dai gano cewa kororon roba yana da tasiri sosai wajen hana
yaduwar wannan cuta a lokacin jima’i. Amma a wasu yankuna da dama na duniya,
maza ba su so, ko kuma ba zasu iya amfani da kororon ba.
A
yanzu, wani sabon bincike ya nuna cewa wani man shafawa na kashe kwayoyin cuta
mai kashe kwayoyin HIV, yana iya hana mace kamuwa da wannan cuta idan ta tara
da namijin dake dauke da cutar. Dr. Lameck Chinula yana aiki ma Jami’ar
carolina ta Arewa a wata cibiyar da ta kafa a kasar Malawi.
Dr.
Chinula ya ce, “Ana shafa wannan man kashe kwayoyin cuta a farji ko a dubura
domin rage yiwuwar kamuwa da kwayar halittar cuta ta HIV mai janyo kanjamau.
Wannan kuwa yana da matukar muhimmanci musamman a kasashe irinsu Malawi inda
akasarin mata ba su da zabin sanya mazaje su yi amfani da kororon roba.”
Chinula
yana cikin gungun wasu masana kimiyya na kasa da kasa da ake kira “Microbicide
Trials Network” masu bincike kan man shafawa mai kashe kwayoyin cuta. Masu
bincike a kasashe biyar sun bayar da man shafawa na kashe kwayoyin cuta ga mata
su fiye da dubu uku domin su yi amfani da shi na tsawon shekara daya da rabi.
A
lokacin gudanar da wannan binciken, an ba wasu matan man shafawa dake dauke da
maganin kashe kwayoyin cuta, wasu an ba su man dake dauke da wani sinadari na
toshe kafar shigar kwayar cutar HIV, wasu kuma an ba su man da babu wani magani
a ciki amma ba tare da sun san hakan ba. Har ila yau, an ba su kororon roba,
aka yi musu jinyar duk wata cutar da suke da ita wadda ake dauka ta jima’i, aka
kuma sanar da su yadda zasu iya hana kawunansu kamuwa da kwayar cutar HIV.
Dr.
Chinula ya ce, “Mace zata shafa wannan mai idan ta san cewar zata tara da
namiji a ranar, ko kuma zata shafa ba tare da bukace shi da yayi amfani da
kororon roba ba.”
Daya
daga cikin abubuwan da aka gano shi ne wannan mai bai kara kasadar mace ta
daukar kwayar cutar HIV kamar yadda gwajin farko da aka yi can baya da
irin wannan mai ya haddasa ba. Chinula ya ce la shakka, wasu daga cikin matan
da suka karbi man shafawa mai dauke da maganin kashe kwayoyin cuta sun dauki
kwayar cutar ta HIV, amma yawansu bai kusanci na sauran matan da ba su shafa
irin wannan mai ba.
Ya
ce, “ba mu da wadatacciyar shaidar da zamu bugi kirji mu ce wannan mai yana
hana mace daukar kwayar cutar HIV, amma ina da kwarin guiwar cewa shi wannan
mai zai bada wata ‘yar kariya ga mata.”
Chinula
ya ce wannan sakamako na binciken nasu, zai kara muhimmin bayanin da ake bukata
domin gaggauta gano man shafawa na kashe kwayoyin cuta mai kaifi wanda zai zamo
makamin da mata zasu iya amfani da shi nan gaba wajen kare kawunansu.

