Shugabar kungiyar Likitocin Najeriya Dr, Princess Campbell ta bayyana cewa Najeriya na matsayin na 176 daga cikin kasashe 190 na duniya da  suka ci gaba a fannin harkokin kiwon lafiya.

Bisa ga cewar shugabar kungiyar likitocin, ana rasa ran mace daya daga cikin mata goma sha takwas sakamakon matsalolin da suka shafi haifuwa. Dr Campell ta bayyana haka ne a wajen wani taron da kungiyar tayi kan matakan shawo kan mace macen mata masu ciki a dakin taro na Civic Center dake birnin Ikko.

Rahoton asusun tallafawa kananan yara na UNICEF  na nuni da cewa, mata a kasasahe masu tasowa kamar Najeriya suna cikin hadarin mutuwa sakamakon matsalolin da suka shafi haihuwa  kimanin sau dari uku fiye da  wadanda suke kasashen da suka ci gaba. Dr Campbell ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kara maida hankali wajen kula da harkokin kula da lafiya musamman ta mata masu ciki.

An yi kiyasin cewa kimanin mata dubu hamsin da biyar ke mutuwa kowacce shekara a lokacin haihuwa ko kuma ta dalilin matsaloli da suka samu bayan haihuwa. Ta kuma yabawa  kungiyoyi masu zaman kansu da suke bada gudummuwa a yunkurin shawo kan wannan matsalar.