Wani jami’in  yan sandan ciki na Najeriya yace an kama kakamin kungiyar Boko Haram da ake dorawa alhakin hare haren da  suka yi sanadin kashe daruruwan mutane a arewacin Najeriya.

Darektan yan sandan ciki na jihar Borno ya shaidawa manema labarai cewa, an kama kakakin da ake kira Abul Qaqa a Maiduguri. Darektan ya bayyana cewa, an kama Abul Qaqa ne ta wajen bin sawun wayarshi ta salula, ya kuma bayyana cewa, kakakin kungiyar dan Najeriya ne wana.

Aika Sharhinka