Kura ta lafa a kauyen Maza dake cikin karamar hukumar Jos ta arewa a tsakiyar Najeriya,bayan da wasu mahara suka kashe akalla mutane takwas.

Hukumomi sun ce mutanen da suka kai farmakin, sun yi amfani da adduna da  wukake, kuma sun kona  wata majami’a a kauyen da  akasarin mazauna cikinsa  kiristoci  ne,  kusa da Jos. Wan nan tarzomar ta zo ne dab da gama  wata  mummunar arangama a  garin wukari dake gabashin kasar, har aka kashe akalla mutane hudu, a fada tsakanin musulmi da kirista. Tarzoma bisa  sabanin akida ta halaka  darururwan mutane a tsakiyar kasar. A  arewacin Najeriya dai muslmi ne suke da rinjaye, a kudanci kuma kirista.