Rasha wadda ta kasance babbar kawar Syria tace ko kusa  ba zata bari a tura sojojin kasashen waje cikin kasar Syrian ba. Rasha ta bayyana haka ne yayinda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yake muhawara kan hanyoyin shawo kan rikicin da ya kai wata 10,  na nuna rashin amincewa da mulkin shugaba Bashar al-Assad.

Da yake magana kan wannan batu yau laraba, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, yace kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ba zai goyi bayan duk wani mai niyyar amfani da karfi kan Syria ba

Ya bayyana haka ne kwana daya bayanda manyan jami’an difilomasiyya a kwamitin sulhun suka zauna domin nazari kan daftarin da Rasha tayi wa kwaskwarima, har  take cewa za a dora alhakin rikicin  kasar ta sham  kan gwamnati  da kuma  ‘yan tawaye. Amurka, da Faransa, da Britaniya suna neman kwamitin ya zartas  da kuduri mai karfi da zai soki lamirin gwamnatin Syria, amma Rasha da China sun ki.

A jiya talata Syria tayi watsi  da shawarar da Qatar  ta bayar, na neman a tura sojojin ketare a Syria domin shawo kan zubda jini da ake yi, Syria tana cewa hakan zai kara dagula lamarin, kuma ya bada kafa ga kasashen waje suyi katsalandan a al’amuran kasar.

Shugaban Amurka Barack Obama a jiya talata yayi Allah wadai da ci gaba da matakan murkushe masu zanga zanga da hukumomin Syria suke yi, ya kuma yi alkawrin  kara azamar kasa da kasa na tilastawa shugaba Assad yayi murabus.