Tarayyar turai ta tsaida shawarar  aza takunkumin hana sayen mai daga kasar Iran.

Litinin din nan ne kungiyar mai wakilai 27 ta bayyana daukan wan nan mataki a birnin Brussels a kokarin dakatar  da shirin Iran na habaka makaman Nukiliya.

Ministocin harkokin waje na kasashe dake cikin kungiyar wadanda ahalin yanzu suke taro a birnin Brussel din, zasu zayyana abinda wan nan kuduri zai kunsa.

Wadansu rahotanni suna cewa za a aza aza takunkumin ne daki daki cikin watanni masu zuwa.