Akwai hanyoyi guda uku na yin kofen shirye-shiryen Sashen Hausa na Muryar Amurka:
1. iTunes: Idan kana da iTunes a jikan kwamfutarka, to sai ka matsa aninin da aka rubuta iTunes jiki a karkashin shirin da kake son yin kofe, sai ka bi umurnin da za ka gani na yin kofe ta iTunes.
2. MyYahoo: Idan kana da akwatin Yahoo, zaka iya kofen shirye-shiryen ta amfani da akwatin naka na MyYahoo. Yadda za ka yi, shi ne sai ka matsa aninin da aka rubuta MyYahoo jiki karkashin shirin da kake so, sai ka bi umurnin da za ka gani na yin kofe ta hanyar Yahoo.
3. RSS: Idan ba ka da iTunes ko akwatin Yahoo, zaka iya amfani da kowace irin na’ura mai karbar Podcast ko mai iya karanta labarai da zarar sun fito, RSS. Idan kana da irin wannan na’ura, sai ka yi kofen adireshin dake kasa da shirin da kake so ka sanya cikin na’urar ta ka.
Idan Kana Son Sauraro ko Kallo Ne Kawai A Wannan Shafin
Kana iya sauraro ko kallon duk wani shiri da muke rabawa ta Podcast kai tsaye daga wannan shafin. Ka matsa aninin da aka rubuta Saurara ko Kalla jiki a karkashin shirin da kake so.
Kofin Podcast na Sauti
Shirin Safe
Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.