VOANews.com

Muryar Amurka ▪ Hausa Majiya Kwakkwara

10 Nuwamba 2009 

Yau A VOA:

Labarai Cikin Harsuna 45
  Kunnenku Nawa

Sai Bango Ya Tsage
Wannan fili ne dake gayyato shugabanni da manyan jami’ai dake bisa wani mukami domin su amsa tambayoyin jama’a talakawa kan irin amanar da aka damka musu. A wasu lokuta kuma, a kan hada kwararru domin su fasa bakin wani batu mai muhimmanci ga masu sauraro.

Masu sauraro suna iya kiran Sashen Hausa kafin shirin domin su ba mu lambobin wayar da zamu kira su a kai, ko kuma su aiko mana da lambobinsu ko tambayoyinsu ta hanyar E-Mail.

Lambar Sashen Hausa: +1-202-203-4077
Adireshin Email: 
hausa-service@voanews.com

RANA: Jumma'a, Karfe 2030-2100 UTC (9:30-10:00 pm Agogon Nijeriya)

Ra’ayoyin Masu Sauraro
A cikin wannan fili, masu sauraro suna iya bayyana ra’ayoyinsu, ko shawarwari, a game da shirye-shiryen Sashen Hausa na Muryar Amurka. A bayan wannan, mai sauraro yana iya aikowa da ra’ayinsa kan harkokin siyasar kasarsu, ko wani batu dake shafar al’ummar duniya, ko yin sharhi mai ma’ana ba na zagi ko cin zarafin wani ba.

RANA: Alhamis, Karfe 1500-1530 UTC (4:00-4:30 pm Agogon Nijeriya)

Karamin Sani, Kukumi
Wannan shiri yana gabatar da rahotanni na musamman kan yaki da cututtuka masu addabar matasa, kamar Kanjamau ko AIDS ko kuam SIDA, tarin fuka da sauransu. Haka kuma filin yana tabo sauran batutuwan da suke addabar matasa a wannan zamani. Sannan kuma, akwai jerin wakoki guda goma da suka fi farin jini a Amurka cikin wannan makon. Abin dai babu kama hannun yaro...

RANA: Asabar, Karfe 1800-1830 UTC (7:00-7:30 pm Agogon Nijeriya)

A Bari Ya Huce...
Hausawa suka ce, “a bari ya huce, shi yake kawo rabon wani.” Wannan fili nme dake kawo labarai na ban mamaki, ko ban dariya, ko ban haushi, ko na shirme! Ana kuma gaurayawa tare ad wakoki daga kowane lungu na duniya, tare da mika gaishe-gaishe ga wadanda suka rubuto wasiku zuwa ga wannan gidan rediyo.

RANA: Asabar, Karfe 0500-0530 UTC (6:00-6:30 am Agogon Nijeriya)